Kwararrun masana kwallon Turai na komawa Saudiyya

Kwararrun masana kwallon Turai na komawa Saudiyya
View on original source
Category: Sports
Share
Archive
Like
A jiya Lahadi ƙungiyar Al Hilal da ke Saudiyyan ta ƙulla yarjejeniya da Richard Hughes a matsayin sabon darakatan wasanninta, matsayin da a baya-bayan nan ya riƙe a ƙungiyar Liverpool, ƙungiyar da ya fara aiki da ita a shekarar 2024, bayan da ya rabu da Bournemouth. Richards Hughes ne ya zaɓi Arne Slot a matsayin kocin da ya maye gurbin Jurgen Klopp bayan ƙarewar yarjejeniyarsa. Kafin ƙulla yarjejeniya da Hughes, Al Hilal ta ƙulla yarjejeniya da ƴan wasan da suka haɗa da Gabriel Martinelli daga Arsenaal, da Crysencio Summerville daga West Ham, sai kuma Ollie Watkins daga Aston Villa, duk a wannan sabuwar kakar wasa. Fiorentina da ke gasar Seria A ta kori Kocinta Fabio Grosso a jiya Lahadi, bayan da ƙungiyar ta sha kashi a wasanni uku da ta buga a jere bayan fara sabuwar kakar wasa. Wasannin uku kuwa da Fiorentinan ta ji jiki sun haɗa da lallasa ta da 4-0 da As Roma ta yi, sai kaye 3-0 da ta sha a hannun sabon shiga Frosinone, yayin da kuma a ranar Asabar da ta gabata, Torino ta zo har gida ta samu nasara kansu da 2-1. Duka-duka dai Fabio Grosso bai wuce watanni uku da karɓar aikin horas da Fiorentina ba kan yarjejeniyar shekaru 2, inda ya maye gurbin Paolo Vanoli. Belgium ta zama ƙasa ta baya-bayan nan da ta janye goyon bayan da ta ke bai wa shugaban FIFA Gianni Infantino, sai dai a wannan karon na ta dalilin ya sha banban da na masu neman ya sauka daga muƙaminsa saboda yunƙurinsa na neman saida wani kason hannun jari ga 'yan kasuwa, manufar da ake zarginsa da son rai akai. Cikin sanarwar da ta fitar, Belgium ta ce sharaɗin janye matakin da ta ɗauka shi ne shugaban, ko hukumar ta FIFA ba ta yi mata bayani gamsasshe a kuma gabatar da hujja karɓaɓɓiya a kan dalilin da ya sa aka janye jan katin da aka bai wa ɗan wasan Amurka Folarin Balogun a yayin gasar cin kofin Duniya ta bana da aka kammala a Amurka. A cewar hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ta Belgium tana son FIFA ta sanya neman bahasin taƙaddamar a cikin batutuwan da za a tattauna akai yayin taron majalisar ƙoli na hukumar ta FIFA da zai gudana ranar 15 ga watan Oktoba da ke tafe. Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce bajintar da suka yi wajen samun nasara kan Chelsea da 2-1 a jiya Lahadi, 'yar manuniya ce kan cewa za su iya taka rawar da ta zarta wadda suka yi a kakar wasan da ta ƙare har ta kai su ga lashe kofin gasar Firimiya karo na farko cikin fiye da shekaru 20. A can Spain kuma, kocin Real Madrid Mourinho Jose Mourinho ne ya ce ko kaɗan babu wata matsin lamba da yake fuskanta, ko kuma damuwa cikin ransa kan cewar tilas sai ya lashe kofin gasar zakarun Turai, a lokacin da zai shafe tare da ƙungiyar ta Real Madrid da yake jagoranta a karo na biyu. Mourinho ya yi kalaman ne gabanin karawar da za su yi da Inter Milan a wasansu na farko da za su buga na gasar ta cin kofin zakarun Turai a gobe Talata. LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye. Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

(0)Comments

 

A note on cookies

Newshunt uses essential cookies to keep you signed in and to remember your language and country, so the site works the way you expect. With your permission, we'd also like to use analytics cookies to understand how people use Newshunt and improve it over time.

Accepting only affects analytics. To learn more, view our Privacy Policy or Terms & Conditions.