Rasha: Huldar diflomasiyya da Jamus ta rushe?

Rasha: Huldar diflomasiyya da Jamus ta rushe?
View on original source
Category: Blend
Share
Archive
Like
Rasha ta sanar da shirinta na rufe ofishin jakadancin Jamus a St. Petersburg da kuma duka cibiyoyin al'adu da koyon Jamusanci na Goethe a kasar, a wani mataki na martani ga Jamus. Ma'aikatar harkokin kasashen wajen Rasha ce ta sanar da hakan, inda ta umurci dukkan ma'aikatan Cibiyar Goethe da su fice daga kasar nan da ranar 13 ga watan Satumba na 2026. Haka kuma Moscow ta umurci ma'aikatan ofishin jakadancin Jamus, su bar kasar nan da ranar 18 ga watan na Satumba. Wannan na zuwa ne, bayan da Jamus ta rufe Cibiyar Koyar da Al'adu ta Rashada ke Berlin da kuma ofishin jakadancin Rashan a Bonn. Jamus ta dauki matakin ne bayan ta dora alhakin wani yunkurin hari da abubuwa masu fashewa a watan Agustan 2026 a kan Moscow. Lamarin dai ya afku ne, a filin jiragen sama na birnin Leipzig. Tuni dai shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana matakin na Jamus da mummunan kuskure, tare da zargin Berlin da yadda da shaidun da aka kirkira.

(0)Comments

 

A note on cookies

Newshunt uses essential cookies to keep you signed in and to remember your language and country, so the site works the way you expect. With your permission, we'd also like to use analytics cookies to understand how people use Newshunt and improve it over time.

Accepting only affects analytics. To learn more, view our Privacy Policy or Terms & Conditions.