Sana'ar Lorna Fidelia ita ce dakon juna-biyu. Ta haifa wa wasu mutane ƴan-uku a kwanakin baya, yanzu kuma tana shirin sake ɗaukar wani cikin.
Lorna na cikin matan da suka rungumi wannan sana'a domin su tallafa wa iyalan da suka kasa samun haihuwa.
"Na zauna na yi tunani, kasancewar na kwashe shekaru a matsayin gwauruwa wadda ta haihu. Ina tunanin yadda zan kula da kaina da kuma yarana. Nakan yi aiki duk da cewa ɗan kuɗin da nake samu bai taka kara ya karya ba''.
"Amma akwai wasu mutanen waɗanda Allah Ya hore musu, suna da abinci suna iya biyan kuɗin haya da na makarantar yara, amma ba su samu haihuwa ba. Sai na ga cewa ai zan iya taimaka wa irin waɗannan mutane su samu haihuwa, sannan ni kuma su taimaka min na kula da yarana," in ji Fidelia.
Kafin ɗaukar cikin, mutanen da za a yi wa dakon ciki da kuma wadda za ta yi dakon cikin za su sanya hannu kan yarjejeniya.
A cikin yarjejeniyar za su amince da kuɗin da za a biya ta da kuma cewar ɗan da za ta haifa nasu ne, saboda haka ba za ta riƙe shi ba.
Daga nan sai a fara batun dasa mata ɗan tayi a mahaifa.
A asibiti, likita zai ɗauki maniyyin miji da ƙwan matarsa, sai a yi gwaji a tabbatar da lafiyar wadda za ta yi dakon cikin, daga nan sai a dasa mata ƙwan a mahaifa.
Dr. Susan Karanja, likita wadda ta ƙware kan dashen ciki a Asibitin Nairobi West ta ce a Kenya, ya kamata macen da za ta yi dakon ciki ta kasance daga shekara 25 zuwa 45 da haihuwa kuma wajibi ne a yi mata gwaje-gwaje kafin a amince da ita.
"Ana yi wa wannan matar gwaje-gwajen lafiya domin ganin ko tana da lafiya, ko jininta lafiyarsa ƙalau, da zarar mun kammali likita zai kuma duba maihaifarta domin ya tabbatar komai lafiya ƙalau.
"Daga nan za mu ɗebi maniyyin namiji da ƙwan matarsa mu haɗa su, sai mu kwantar da wadda za ta yi dakon cikin mu dasa ƙwan a mahaifarta."
Bayan an yi dashen za a buƙaci mai dakon cikin ta huta sosai, ta guji yin aikin wahala saboda kada cikin ya zube.
Matar da ke dakon cikin za ta samu kuɗi, kasancewar iyayen jaririn za su riƙa biyan ta albashi duk wata sannan kuma za su riƙa samar mata duk abubuwan da take buƙata. Lorna ta samu duk waɗannan abubuwa a lokacin da ta yi dakon ƴan-uku.
"Idan akwai wani lokaci da na kasance hankalina ba ya tashi kan samun abinci da biyan kuɗin makarantar yara da kuɗin haya, to a lokacin ne," in ji ta.
Kuɗin da ake biyan mata masu dakon ciki a Afirka bai taka kara ya karya ba idan aka haɗa da wanda ake biyan masu irin wannan sana'a a ƙasashen da suka ci gaba.
Misali, a Amurka mace mai dakon ciki za ta iya samun kuɗin da ya kai tsakanin dala 120,000 zuwa 220,000 a duk ciki ɗaya da ta rena, wato kimanin naira miliyan 158 zuwa miliyan 290.
A Kenya, doka ba ta wajabta biyan wani ƙayyadajjen farashi ba, sai dai kawai ya zama tamkar kyautatawa ce da iyayen jaririn za su yi wa mai dakon cikin, wanda yakan kama daga ƙaranci dala 1,000 zuwa dala 8,000, wato kimanin naira miliyan 1.3 zuwa naira miliyan 10.
Akwai asibitocin neman haihuwa kimanin 15 a Nairobi, babban birnin Kenya.
Dashen ɗan tayi da dakon ciki ya fara yawaita a nahiyar Afirka bayan raguwar da aka samu na samun juna-biyu da kashi 37%.
Duk da cewa Lorna ba ta taɓa fuskantar barazana ba, wasu masu dakon cikin sun riƙa fuskantar hantara daga dillalan da ke haɗa su da ma'auratan da ke neman masu dakon-ciki.
Ya kasance dillalan suna karɓar kuɗaɗe masu yawa daga wurin iyayen jaririn amma ba su bai wa masu dakon cikin kuɗin da ya kamata.
Haka kuma wani lokaci akan samu saɓani tsakanin iyayen jaririn da kuma masu dakon cikin.
Ayieta Lumbasyo, lauyan da ya shahara a fannin dokokin ɗaukar ciki, ya bayyana cewa rashin rashin samar da dokoki kan haihuwa da kuma rashin ci gaban zamani a ƙasashen Afirka da dama sun sanya ana samun matsaloli.
"Za ka iya ganin cewa wadda za ta yi dakon cikin ba ta fahimci yarjejeniyar da aka ƙulla ba. Rashin dokoki na sanyawa ba za ka fahimci alfanun da za ka samu ba. Ana cutar ƴanmata, ba a biyan su yadda ya kamata...da farko sai a ce za a biya 700,000 daga baya kuma a canza a ce 400,000," in ji Ayeta Lumbasyo.
Ƙasashe kamar Kenya, Uganda da Tanzania ba su da dokokin da suka shafi ɗaukar ciki da haihuwa.
A Kenya akan bar masu dakon ciki da yaro kasancewar ana wa yaro rajista ne da zaran an haife shi.
Amma a yanzu Kenya na ƙoƙarin amincewa da wata doka wadda ta shafi ɗaukar ciki da haihuwa.
Sai dai masanin shari'ar na nuna damuwa: "Matsalar ita ce dokar za ta iya buɗe ƙofa ga mutanen da za su iya satar jarirai. Abin da muke so shi ne su rage wahalar da ake sha wajen ganin iyaye sun karɓi yaransu."
Duk da tsangwama da masu matsalar haihuwa ke fuskanta, yin amfani da cigaban zamani wajen samun haihuwa na ci gaba da samun karɓuwa a nahiyar Afirka, to sai dai matuƙar babu dokokin da za su tafiyar da fannin, za a ci gaba da fuskantar matsaloli.
(0)Comments