Mataimakin shugabar, Deogratius Ndejembi ne ya sanar da rasuwar a hukumance, yana mai cewa, marigayin ya jima yana fama da cutar zuciya, kuma ya rasu yana da shekaru 77a duniya.
Tuni wasu shugabannin suka fara miƙa saƙonnin ta'aziyarsu ga Samia da al'ummar ƙasar Tanzaniya, yayin da ake shirye-shiryen Jana'izarsa a ƙauyensu na Kizimkazi da ke birnin Zanzibar.
Marigayi Ameir, ƙwararren masanin tattalin arzikin noma ne kuma matarsa ta zama shugabar ƙasa bayan lashe zaɓen watan Maris na 2021.
Sun yi aure da matarsa a shekarar 1978 kuma suna da ƴaƴa huɗu da suka haɗa da maza 3 da mace guda.
Marigayin ya taɓa riƙe kujerar mamba a majalisar wakilan Zanzibar.
Shugaban Kenya, William Ruto na daga cikin waɗanda suka fara mika sakon ta'aziyarsu a shafinsa na X,inda ya ce Dokta Samia, ta rasa abokin zama kuma uban ƴaƴanta amma Kenya na tare da ita a wannan lokaci na jimami.
Shi ma shugaban ƙasar Burundi Évariste Ndayishimiye, ya miƙa nasa saƙon ta'aziyar. Kazalia Shugaban Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta AU, Mahmoud Ali Youssouf ya aike da nasa saƙon ta'aziyar, a madadin ƙungiyar ta AU gami da fatan Alllah Ya ƙara dangana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI
(0)Comments